4 Afirilu 2022 - 19:24
Sama Da Bakin Haure 90 Ne Suka Mutu A Wani Sabon Bala’I Da ya Afku A Tekun Medetereniya

.A cikin wani bayani da Shugaban Hukumar kula da yan gudun hijira na Majalisar dinkin duniya Filippo Grandi ya wallafa a shafinsa na twita ya fadi cewa sama day an gudun hijira ba bisa ka’ida ba 90 ne suka hada da jalinsu a tekun Medetireniya, kana ya saki matakan harshen da kasashen turai suke dauka kan batun yan gudun hijira

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace kasashen turai sun sanar da karfinsu na iya karbar yan gudun hijira miliyan 4 daga kasr Ukrain domin kyautatawa, cikin gaggawa , to amma me ya sa ba za su nuna irin wannan shirin na karbar yan gudun hijira da suka kwankwasa musu kofa ba daga wasu kasashen duniya.

A ranar Asabar da ta gabata Likitocida basu da iyaka sun sanar da mutuwar yan gudun hijira guda 90 bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a cikin tekun kasa da kasa na Medetireniya, bayan da suka kwashen dogon lokacia gabar tekun kasar Libiya kafin afkuwar wannan hatsarin

Ta kara da cewa tuni aka ceto mutane 4 daga cikinsu, wasu rahotanni sun ce kwale-kwalen yana dauke da dama da mutane 100 , Kasar Libiya da tekun Mdedertiya ta kasance babbar tashar dab akin haure ke amfani da shi zuwa kasashen turai.

342/